Yadda Zakuyi Ajiyar Sakonni da Nombobin ku



Barka da warhaka fatan kuna Lafiya, kamar yadda kuka gani a rubuce yadda zaku ajiye sakonni wato message da ke shigowa a wayarku da kuma Nombobin wayarku da kuma duk wani kira da ya shigo wayarku ta yadda ko kun canja waya zaku iya dawo da dukka sakonni da Nombobin wayarku zuwa sabon wayarku.
Ga yadda zaku yi
Da farko kuyi downloading na wannan App din Super backup.apk bayan kunyi downloading nashi sai kuyi installing sai ku bude ciki zaku ganshi kamar haka


 idan son ku Ajiye sakonnin ku ne sai ku danna Kan SMS, idan ya shiga a sama zakuga BACKUP ALL sai ku danna kai zai kaiku wani waje an rubuta Sms_20******* a kasa akwai Ok sai ku danna, zakuga ya fara Backup din.


 Idan kuma Nombobi kuke so ku ajiye sai ku koma fuskan application din zakuga Contacts a layi na biyu sai ku danna shima a sama zakuga BACKUP ALL Zai kaiku wani waje an rubuta contacts_20***** a kasa kuma akwai ok sai ku danna kai, zai fara backup din, yanzu duk Nombobin ku yana memorin ku. 

Idan kuma kunyi sabon waya kuna so ku dawo da sakonnin da Nombobin na ku, sai ku sake downloading application din, kuyi installing ku bude, idan ku na son ku dawo da sakonni ne sai ku danna kan SMS idan ya shiga sai ku duba zakuga RESTORE sai ku danna, idan ya shiga sai kuje inda aka rubuta sms_20**** sai kudanna duk abunda ya tambayeku ku dinga danna ok kawai shikenan zakuga ya fara aiki, idan kuma Nombobin ku ke son dawowa dasu sai ku danna contacts idan ya shiga sai ku duba zakuga RESTORE sai ku danna, idan ya shiga sai kuje inda aka rubuta contact_20**** sai kudanna duk abunda ya tamabayeku ku dinga danna ok kawai shikenan zakuga ya fara aiki.
To da wannan bayani nawa ina fatan zaku iya ajiye sakonni kuma ku dawo dasu. 

Shin baku da memorin da zaku iya ajiyar?
To ko kun san zaku iya ajiyar a website namu na Elguduwis Tech? 
Ta yaya zakuyi ajiyar? 
Ku biyoni a post nawa na gaba. 
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment