Yadda Zaku Gyara Application Na Hoto



Kamar yadda kuka sani kwana baya kwanan baya na yi bayani yadda xaku bude account a andromo idan baka karanta to sai ka fara karantawa ta nan:- Yadda Zaku Gyara Application kashi na daya(1)


To yau zamu yi bayani kan yadda zamu gyara application na hoto.

Kafin in fara, gaskiya a bayani kadai ba zai yiwu ku fahimce ni ba, abun da nake so shine ku fara karanta post din da zanyi a kasan shi akwai video sai ku kalla videon sosai akwai kuma wajen da zakuyi downloading na videon. 

Da farko ku shiga browsern ku (Ina bada shawarar kuyi aiki da chrome) sai ku shiga www.Andromo.com ku duba sama ta hannun dama zakuga wani gu kamar option, sai ku danna idan ya fito zakuga Login a Kasa sai ku danna zai kaiku inda zaku saka email da password na ku wanda kuka bude Andromo da shi, bayan kun saka sai ku danna Login, Idan ya shiga za kuga application na ku da sunan da kuka saka sai ku duba gefensa zakuga wani waje An rubuta Action, Idan kuka danna, kuna dannawa zakuga wani waje ya fito a samanshi an rubuta Edit Project  sai ku danna zai kaiku wani waje ku duba zakuga settings sai ku danna kai bayan kun danna sai ku tafi kasa zuwa inda aka rubuta App Icon. A wurin zakuga Tambarin Andromo (Wato Shine Hoton da yanzu yake kan application na ku)  sai ku canja kuka wanda kuka so ta hanyar danna idan kun danna Sai kuje ku zabi hoton da kuke so ya zama hoton application na ku din sai ku danna kai bayan kun danna sai ku je Kasa inda aka rubuta save changes bayan kun danna idan ya gama loading zai mayar da ku sama sai ku duba inda aka rubuta Activities sai ku danna shi, ku na danna shi sai ku dan ja kasa zakuga inda aka rubuta +Add an activity sai ku danna shi, zai watso muku abubuwa da yawa Sai ku ɗan jashi (Wannan Abubuwa da suka fito)  kasa har sai kun xo inda kuka ga an rubuta Photo Gallery sai ku danna, idan kun danna ya gama loading a sama zakuga Activity Name sai ku rubuta sunan abun da za ku sa ka, misali tunda hotuna zamusa sai ku saka "Sunanku Pictures" sai ku ja kasa zakuga Save Changes sai ku danna idan ya gama loading zai kaiku wajen da zaku saka hotunan ku ta hanyar danna , sai kuje Foldan hoton ku, sai ku zabi hoton da kuke so ku sa a cikin Application kwaya daya idan kuka danna sai ku tafi kasa zakuga save changes idan ya gama loading sai ku sake tafi ya kasa sosai zaku zo Inda zakuga hoton da kuka sa ka dazu, a kasanshi akwai +Add Photo sai ku danna idan ya gama loading sai ku maimata yanda kuka yi na farko ha ka zakuyi tayi har sai hotunan ya ishe ku.
Idan kun gama saka hotunan sai kuje kasa za kuga save changes sai ku danna idan ya gama loading zai kaiku sama, a sama zaku ga Build sai ku danna, idan kun danna sai ku duba kasa zakuga Build My App sai ku danna Zai maidaku fiskan Application ɗin,  to sai ku jira a wajen Zuwa minti biyar ko shabiyar (Zaku iya fita ku kashe datan ku) zasu turo muku da sako ta email naku,  idan kuma basu turo ba sai ku koma browsern ku sai ku duba gefen Application zakuga Action sai ku danna a kasa zakuga download sai ku danna idan ya gama  sai kuyi installing nashi.

Ku kalli videon da ke kasa ko kuma kuyi downloading ta nan: Yi Downloading 

Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment