(Airtel) Yadda Zaku sa kati kuyi Amfani dashi ko ana binku Bashi A Layinku


Sanin kanku ne idan kun karbi bashi a Layin ku na Airtel, ba dama ku sa kati kuyi Amfani dashi, domin kuna sa ka katin zasu cire kudin su. Kamar masu aiki da airtel nasu a bankin su. Ba za ku iya komai a bankin ku ba sai da kudi a layinku, kuma in suna binku bashi sai kun biya su kun sake sa kati tukunna kafin kuyi wannan. Mutane da yawa sun sha tambaya ta kan wannan batu amma basu samu amsa ba sai yanzu da nayi bincike na jarraba sai na samu amsar tambayar ku. 

Toh idan kun ci bashi a layin Airtel kuma kuna Bukatar kusa kati ba tare da sun janye katin nasu ba, ga yadda zakuyi. 

Da farko kuna bukatar wani layin zain domin yin hakan, zaku iya aron wayar wani domin yin hakan sai ku saka katin da kuka saya  ta hanyar *126*Pin# a layin da babu bashi a ciki. Idan ya shiga sai ku yi transfer wato (2u) zuwa layin da ake binku bashi. Ma'ana ku tura katin da kuka saka a dayar layin zuwa layin da ake binku bashi. Shikenan idan ya gama ya tafi, sai ku duba balance naku zakuga kudinku na nan ba su taɓa ba.
Fatan kun Fahimce ni.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment