Yadda Zaku Kalli Hotuna Ko kuna Free Mode (Free Basic) A Facebook

Kamar yadda kuka sani, idan datan ku ya Qare,  zaku iya shiga facebook kuyi chatting wato ta free Mode ko free basic, amma banda kallon hotuna, ma'ana baza ku iya kallon hoto idan wani yayi posting ba, so a wannan rubutu zan nuna muku yadda zaku iya ganin hoto a facebook ko kuna Free Basic wato ko babu Data a wayarku.
Ga yadda Zakuyi:
Da fari kuyi downloading na facebook Lite App Ta nan  Idan kuma kuna da shi shikenan bayan kunyi installing kun bude sai ku yi Login Na Facebook naku, idan ya shiga ya nuna muku kuna free mode wato zaku iya Ganin Posting na mutum amma banda hoto, sai ku kashe datan ku, ku fita daga cikin application din sai kuje Setting idan kuka shiga ku Nemi wani waje da aka rubuta Apps ku shiga,ku nemi Application mai suna Lite sai ku danna kai, idan ya shiga zakuga Clear Data sai ku danna kan shi.
[A wayar da ta kai version 6 ko 7 ga yadda zaku yi, ku shiga settings sai ku je kan Apps sai ku nemi Application mai Suna Lite sai ku danna kai zakuga storage sai ku danna, yana shiga zaku ga manage Space sai ku danna zakuga wani waje anyi marking wani kuma ba'ayi ba, sai ku tabbatar cewa dukka kunyi marking Na su, Za ku ga CLEAR sai ku danna Kai Shikenan]

Idan kun gama sai ku koma application na facebook Lite din Sai ku Sake Saka Nombar wayanku Da Password idan ya shiga.
      Shikenan zakuga kuna iya ganin Hotuna Kuma ba data a wayarku, amma ba za ku iya kallon Video  ba.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment