Menene Banbancin Email Da kuma Gmail?

Barka da war haka fatan kuna Lafiya .
Mutane na yawan mini tambaya cewa wani lokaci idan na yi posting su kan ga na sa "Sai ku Sa Email Naku a wajen" shine suke nuna su ba su da email sai gmail.
A yau ina so in Fayyece muku menene wadannan ababe biyun. 

Da Farko Email na nufin Electronic Mail . Email zan iya ce cewa kamar general name ne na duk wani sako da za'a tura ta hanyar Amfani da electronic mail, idan nace general name ina nufin sunan gama gari.
Duk wani link ko address da kaga @ aciki to wannan sunan shi email ne. 
Shi kuma gmail na nufin google mail, Google kamar yadda kuka sani sunan Company nine, Kamar yadda akwai yahoo mail da sauran su duk sunan su email wato email shine general name nasu,  Kamar SIM CARD ne , akwai MTN, Airtel, Glo da sauransu dukka Sunan su Sim CARD ne amma ko wani kampani da nasa sunan.

Fatan kun fahimce wannan karamin bayanin nawa. 
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment