Yadda Zakuyi Saurin kama barawon wayarku


Yau zan nuna muku hanyar da zaku yi saurin kama barawon wayarku ka fin yayi nisa.
Wani Abu ya taba samuna a makaranta, Na saka wayata a caji mun kwanta da safe na tashi na samu SIM cards nawa a inda na a jiye wayar,  wani ya sace wayar amman ya ajiye sim din ya tafi da memori na da kuma wayar. Abubuwa masu muhimmanci ya Tafi dasu wanda na ce gwara ya hada da Sim din ma ya Tafi da shi.
Irin abubuwa haka sukan Faru ko kuma ka ajiye wayarka wani don yasan security ko kuma wayar ba security ya dauka yayi abun da yaga dama. Ko kuma kana cikin jama'a wayarka a aljihu wani ya sa hannu ya sace.
To da Yardar Allah wannan zai kare.

Da farko dai dauko app din Mai suna "Anti thieft Alarm" a nan Download ko kaje play store.
Bayan ka bude app din ka saka Nambobin Sirri (password) guda hudu ko kuma pattern, domin yayin da wayar ta fara ihun barawo sai an saka wannan password din zaya dena.
Ga yadda tsaron yake:
1.Charger detention Mode: Wannan tsaro ana sashi ne yayin da kasa wayarka a chaji, da zarar an cire ta daga chajin zatayi ihun barawo,Wannan tsaron yana da Muhimmanci saboda dole in za'a sace wayar sai an cire ta daga chajin.
2.Motion detection Mode: Shi wannan tsaro ana saka shi ne yayin da zaka ajiye wayarka, da ka saka shi sai ka ajiye ta, da zarar an motsata koda da nisan 5cm ne zatayi ihun barawo.
3.Proximity detection Mode: Wannan tsaron ana saka shi ne yayin da kasa wayarka a Aljihu, da zarar wani ya kai hannun sa kusa da aljihunka da nisan 4cm wayar zatamar ihun barawo.
4.Sim detection Mode: wannan tsaron yana bukatar ka bude Wifi na wayarka domin app din yayi detacting na location naka, Sannan kuma kayi register da nambar ka da Email, da zarar an chanja wa wayar layi zata yi ihun barawo ta da ita.

Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment