Yadda Ake Hada Application (1)
kwanan Baya Nayi Rubutu kan Yadda Zaku Gyara Application Naku na kanku, amma saboda Andromo sun canza features na su zamu sake Komawa domin farawa daga farko.
Da fari kuna Bukatar Browser mai Kyau (Kuyi Amfani da Chrome) sai ku rubuta www.Andromo.com sai ku danna go, idan ya gama Loading ya kawo ku homepage na Andromo sai ku scrolling Kasa a hankali, zakuga inda aka rubuta CREATE FREE ACCOUNT
sai ku danna kai, sai ku dan dakata zakuga SIGNUP page ya fito a ciki zakuga:
USERNAME
EMAIL
PASSWORD
REPEAT PASSWORD
Da fari akwai Username: wato sunan da zaku yi amfani dashi a site nasu, sai ku zabi suna sai dai idan zaku rubuta sunan ku ya zama da kananan haruffa tun daga farko har karshe misali "elguduwis" haka ake so ya kasance ba tare da anyi Amfani da manyan Harrufa ba. To bayan wannan sai Email naku, sai ku rubuta email domin ta email naku ne za'a turo muku application din da kuma sauran muhimman abubuwa, ayi kokari asa email mai kyau idan ba haka ba babu abunda zai yiwu.
To bayan wannan sai password, wato nombar sirri, sai ku saka wanda zaku tuna kar ya kasa nomba ko haruffa takwas(8), sai ku je rukuni na gaba za kuga password confirmation, to anan ana so ne a maimata password da aka sa a sama. A kasa kuwa akwai wani box a gefen zakuga an rubuta by signing up You accept.....
Sai kuyi Ticking na Box din, kar ku manta, kuyi Ticking na Box din.
Sai ku danna Signup
Idan ya Gama processing zai kaiku wani page zakuga an rubuta please Verify Your Email
To anan sai ku shiga Email naku zaku ga sako daga Andromo
Sai ku shiga cikin sakon ku duba kasan zakuga CONFIRM EMAIL ADDRESS »»
Idan kuka danna Ya Gama Loading zai kawo ku filin LOG IN >> sai ku saka email da kuka yi Register da shi sai kusaka password da kuka yi registration dazu sai ku danna Rember me sai LOG IN>>>
Idan ya gama loading wani page zai fito a gefen zakuga alamar cancel X
sai ku danna sai ku danyi scrolling zakuga create New app
sai ku danna idan ya kammala loading zakuga inda zaku sa wa Application naku suna Idan kuka sawa application naku suna sai ku danna Create
yana gama loading zakuga project created a sama .
To kun gama creating Application kenan saura kayan aiki sai a darasin mu na Gaba za muga yadda zamu sawa Application namu abubuwa kamar hotuna audios da dai sauran su
Idan an samu matsala kuna iya contacting dina ta contact page.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin
Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka
https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts
Newer Posts
Older Posts
Older Posts
Main Page











Comments