Yaddu zaku hada hoto mai motsi (GIF)
barkan ku da war haka fatan kuna nan lafiya, na san mun danyi kwana 2 ba mu hadu ba ma'ana ba kuga post ba ina bada hakurin haka
a darasin mu na yau zan nuna muku yadda zaku hada hoto mai motsi ma'ana animated pic, kafin mu fara ga misalin hoto mai motsi a qasa:-
da wannan hoton dake sama na san kun fahimci menene nake nufi da hoto mai motsi sai kuma yadda zaku gyara naku. ku nitsu ka karanta wannan post din ba tare da tsalleke ko kalma daya ba .
da fari kuna bukatar wani application domin hada hoto mai motsi. zaku samu wajen downloading din a qasa a cikin wannan app din zaku iya gyara hoto mai motsi. idan kuka yi installing wannan app kuka bude zaku ga
Gif Camera
Video to Gif
Image o Gif
Record screen to Gif
- idan kuka danna kan Gif Camera wannan zai baku daman ku dauki hotuna da cameran ku sai ku maida shi hoto mai motsi.
- idan kuka danna kan video to Gif wannan zai baku daman ku zabi video a wayarku ku maida shi hoto amma baya wuce minti 1 ma'ana tsayin videon ba zai fi minti dayaba.
- idan kuka danna kan Image to Gif wannan zai baku dama ku zabi hotuna daga wayarku ,ku mai da shi hoto mai motsi.
- idan kuka danna Record screen to Gif wannan zai baku damar daukan videon screen naku sai ku maida shi hoto mai motsi
- idan kuka danna kan Gif Editor idan akwai hotuna masu motsi za ku iya editing nasu ta hanyar rubutu akai da dai sauran su
ku kasance da Elguduwis Tech
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin
Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka
https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts
Newer Posts
Older Posts
Older Posts
Main Page


Comments