Yadda zakayi downloading kowani irin video a YouTube



Kamar yadda Muka Sani, YouTube suna da wuyan downloading, Wani lokaci koda kayi downloading ta cikin YouTube Apk, sai dai ka gani ta cikin YouTube Apk din kawai kuma bazai tura ma Wani ba.
 To anan ina so in mana bayani yadda zamuyi downloading ko wani irin video a YouTube.


Da farko sai Kaje kan browsern ka(uc browser,chrome,opera mini. Etc). Idan ka shiga sai ka rubuta a wajen saka address "www.YouTube.com"

Kana shiga idan ya gama loading zai kawo ka home page na YouTube
Idan ya kawo ka, zaka iya searching na film da kake so kayi downloading.
Sai ka kawai ka Danna videon da kake son

To idan kadanna kan videon da kake so, idan ya shiga, sai ka Danna wajen sa address wato wajen da dazun ka rubuta YouTube.com, idan ka Danna zai nuno ma wasu rubutu, to sai ka ja rubutun baya Har sai ya koma farko inda aka rubuta http://m.YouTube.com............ Idan Kaga haka sai kazo dai-dai wajen da aka rubuta m.youtube

Idan kazo dai-dai wajen m. Sai ka share m. Wato kayi deleting dai-dai m. Kawai, idan ka share kayi deleting m. A wurin daka share m. Sai ka rubuta ss wato "s" guda biyu


Bayan ka rubuta ss guda biyu a wajen da ka share m. To sai ka bashi go wato yayi loading kenan idan ya kammala loading zai kawo ka wajen da za kayi downloading




Shikenan yana kawo ka nan sai ka zabi format na videon wato ko 3gp ko mp4 duk wanda kake so sai ka Danna kan format da kake so zai baka option download ko kuma play online (uc browser) sai kawai ka Danna download


Shikenan da haka za ka iya downloading ko wani irin video a YouTube 


Fatan zai muku Amfani



Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment