(Airtel Users) Shin ka/kin sayi Data A Rashin Sani? Kalli Yadda ake maida data a dawo da kudin
Barka da war haka, kamar yadda kuka ga a rubuce yadda zaku maida data A Dawo muku da kudin ku zuwa layin da aka sayi data da shi a saukake, sai ku biyoni domin ganin yadda Ake abun.
Wani Lokaci Mu kan Sayi Data Cikin Kuskure ko kuma da Sanin mu amma da ga baya mu zo muyi da na sanin sayan Datar ko kuma Irin Auto Renewal Na Data da Mafi Yawancin Service ke yi. Sai kaga mutum ya shiga damuwa sosai Amma A wannan rubutu nawa zan nuna muku yadda zaku maida Data Domin A Dawo muku da kudin ku.
Idan Kun Sayi Data a wayarku kuma kuna son maidawa Domin kudin ku ya dawo sai ku bi wadannan sharruda, da Fari Datan ya zama yayi Awa 24 ko fiye da haka (24Hours)da sayan shi kafin nan, sa'annan ya zama cewa ba'a taba datan ba ( ma'ana ba-ayi Amfani da shi ba)
Idan an cika Sharuddan da aka lissafa a farko abu na gaba shine sai ku dau wayarku ku danna *121*6# idan kuka danna zakuga Datan Da kuka saya , idan na dari ne ko dari biyar ko sama da haka sai ku danna Nombar Da kuka ga Datan ku akai sai ku yi musu reply da nomban Shikenan zakuga sun nuna your Reversal was been treated, sai mu duba account naku ta hanyar danna *123#.Da wannan hanya zaku iya Dawo da kudin ku zuwa Account Na ku ko da yaushe.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin
Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka
https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts
Newer Posts
Older Posts
Older Posts
Main Page
Comments