[UC browser ] yadda Ake Gyara Downloading a UC browser idan ya Nuna link expire Ko failed

UC browser Kamar yadda Kuka ga Sunan, wata Browser  ce Mai matukar Sauri da Kuma daɗin downloading,  sai dai wani lokaci Akan Samu matsala ko damuwa wajen Downloading na file.
Anan ina son inyi bayani ne Game da Yadda zaka  gyara downloading idan ka samu damuwa. 
Abubuwa da suke kawo damuwa wajen downloading  a UC browser :
1. Karancin space A memory (low memory space).
2. Rashin kyaun Network. 
3. Dakatar(pause) da downloading na tsawon kwanaki.
Wannan Sune manyan Dalilai da Sukan kawo Problems Ko matsala na Downloading  A UC browser.

Yadda zaka Gyara  Download  Naka:-

Da Fari idan Ka Sa Downloading, Misali mu ɗauka kana downloading na Application mai Suna uc browser.apk Sai ka fuskanci matsala kamar na Download Failed ko kuma link Expire.


To ga yadda zaka yi
1. Sai ka Dakatar(pausing) Da downloading ɗin.
2. Sai Ka fita a cikin browser din Ka tafi Kan Memory na wayarka.
3. Sai Ka Nemi Folder Mai Suna UcDownloads sai Ka Shiga ciki, kana Shiga zaka ga file da Kake downloading  din. 
4. To abunda Muke downloading  din a wannan post shine UC browser.Apk to idan kagan shi zaka ga wani File a Kasan shi Mai Suna UC browser.Apk.cfg.
5. Sai Ka selecting Na su Ko marking nasu wato UC browser.Apk da UC browser.Apk.cfg sai kayi copy nasu Ka Kaisu wani Folder kayi pasting nasu. Sai Ka fita 
6. Sai Ka koma UC browser kaje wajen Downloading sai Ka Danna Kan downloading  din zai nuna maka re-download to sai Ka Danna Kan re-download din sai Ka barshi ya Fara Downloading  din idan ya Fara sai ka Dakatar(pausing) da shi.
7. sai Ka  fita Ka koma memory Naka sai Ka Shiga  Folder Mai Suna UcDownloads sai Ka selecting  UC browser.apk da UC browser.apk.cfg sai kayi  Deleting  nasu.
8. Sai Ka fita Kaje foldan da dazu Ka yi pasting na Abunda kayi copy, sai Ka sa ke Yin selecting  nasu, sai kayi Cutting nasu Kaje folder Mai Suna UcDownloads sai kawai kayi pasting nasu a wajen.
9. Sai Ka Fita Ka Koma UC browser Kaje wajen downloading  din sai kayi Resuming  nashi.

zaka ga  downloading Naka Wanda yayi failing dazu  ya cigaba daga inda ya Tsaya.

Shikenan!!!

Like  us on  Facebook :-
Elguduwis  Technology 

Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka https://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment