Yadda zaku iya samun Datan Airtel 4.6GB akan N200 da kuma 23GB akan N1000


Fatan Alkhairi
Kwanan biyu zuwa uku nayi rubutu na kan yadda (Airtel Users) zasu samu 4.6GB Akan Naira dari Biyu N200, 23GB Akan Naira Dubu daya N1000
Wasu Da yawa sun samu Amma wasu har yanzu. To karku damu.
Abunda zaku yi shine ku dauki wayarku sai ku danna *312# sai ku sake danna 1  Domin komawa tsarin Airtel Trybe.
Bayan sun turo muku sako cewa kun koma tsarin Airtel Trybe.
Toh, sai ku tura GET zuwa 141, sai ku jira saqo cewa Dear Customer, You Can Now Enjoy 100%............

Shikenan sai ku sayi katin Airtel na 200 sai ku Loda ta hanyar danna *143*Nombar recharge card#
Shikenan Insha Allahu zaku samu 4.6GB.

Yanda ake duba datan.
  Ku danan *223# domin ganin datan ku.
Wasu sunce su kan samu 200MB maimakon 4.6GB toh kuma karku damu abunda zakuyi shine
Ku danna *141*6# zakuga datan ku 4.6GB zaune Abunshi.

Idan duk kunbi wannan hanyar kuma  baku samu ba toh Abinda zakuyi shine ku cire sim card naku sai ku nemi karamar waya kamar Nokia, ko dan karamin tecno sai ku tura GET zuwa 141, ku jarraba insha Allah shima za'a dace.

#Elguduwis
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka http://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

1 comment

  1. Sai dai a Halin yanzu sun kulle wannan Hanyar. Amma ba mu san Ko zuwa gaba ba.

    ReplyDelete