Menene Rooting ? kuma menene Amfani da rashin Amfanin sa ga waya

Fatan alkhiari gareku, yau ina so inyi magana akan rooting na wayar android.

Menene Rooting?

Rooting wata hanya ce dake baiwa masu Amfani da android, tablets damar canja asalin system features na waya, idan nace system features ina nufin kamar canja saitin da waya ta fito dashi, wato asalin saitin da waya ta fito dashi ko kuma bada damar canja ko kara space din internal storage. zan kawo muku Amfanin rooting domin ku gane menene asalin dalilin yin rooting din.

Amfanin rooting

Amfanin rooting na da yawa sosai Amma ga daga mafi muhimmancin ciki:
1. Rooting na karawa internal memory space: Wani lokaci idan mutum yayi wiping wayarsa wato ya formatting wayarsa, idan ya lura zai ga wasu Applications sun zo kuma da babu su a wayar  lokacin da zaiyi formating din, toh daga ina suke? wadannan Applications suna cikin asalin root folder na wayar, kuma suna matukar cin space na waya  ba ta yadda za'ayi agansu sai anyi rooting na wayar, toh idan akayi deleting nasu ana samun space sosai a wayar.
2. Rooting na kara wa wayar sauri: Hakika yin rooting na waya na kara wa wayar da aka mata rootiong sauri, wani lokaci mutum zaiga wayarsa na delay ko kuma hanging ma gaba daya, toh meke kawo haka? Mafi asalin dalilin hakan shine sakamakon wasu systems apps da suke running, toh yin rooting na waya zai baka damar dakatar da wadannan system running apps, toh sanadiyar dakatarwar sai ya karawa waya sauri sosai.
3. Rooting na bada damar installing apps da yawa: Yin rooting na wayar ka zai baka damar installing applications masu yawa ba tare da wayarka tayi slow ba, wani lokaci zakaga da kayi installing Apps da dan yawa kadan zaka ga wayarka na delay sosai, toh yin rooting ne zai baka damar installing apps ba tare da slowing wayarka ba.
4. Rooting na bada damar installing special  apps: Akwai wasu apps da aka developing domin baiwa waya kariya, sai dai yin rashin root permission na hana su aiki a waya, da wasu applications kamar na karawa waya RAM, hakika yin rooting zai baiwa wadannan Applications damar yin Aikinsu.

      wadannan sune kadan daga cikin muhimmancin rooting.

Rashin Amfanin Rooting

Hakika komai a duniya nada Amfani kuma yana da rashin Amfani
    Yin rooting na da hatsari  sosai daga ciki akwai:
1. Rooting kan jawo mutuwar waya: yin rooting kan jawo maka asara ta yadda zai kashe maka waya ya maida ta gwangwani, lokacin da kayi rooting akwai asalin system apps da suke controlling wayarka toh taba wadannan apps kan jawo mutuwar waya gaba daya.
2. Rooting na kawo virus: A kwallon kafa akwai defenders wato masu tsaron gida wanda suke kokarin hana cin kwallo, hhh to hakika a waya ma akwai wadannan defendu sai dai wadannan defendu ba ball suke karewa ba suna kare wayarka daga virus, hakika virus na da hatsari domin ko shi kadai kan kashe waya. tohbyin rooting na waya na iya dakatar da wadannan defendun wanda hakan kan kawom maka virus sosai wayarka .
3. Rooting na rage performance na waya: duk da cewa dalilin yin rooting shine karawa waya sauri, amma wani lokaci ya kan jawo delay ga wayar sosai
4. Rooting na rage karfin battery: idan applications suka yawa a waya toh gaskiya karfin batirin wayarka zai ragu sosai.
            wadannan sune manyan hatsarin da rooting kan kawo, amma wadannan Hatsari  suna faruwa ne idan aka samu kuskure,

Hakika yin rooting na waya na da Amfani sosai, sai dai Abun da zai kawo mutuwar waya ba abun wasa bane
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka http://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment