Yadda zaku bude website a Xtgem

Barka da sake kasencewa dani a yau. a wannan rubutu zan nuna muku yadda zaku bude website a xtgem. idan kana cikin masu son bude website to ga hanya:-
Da farko ku shiga browsern ku sai ku shiga www.xtgem.com  bayan ya shiga zai kawo ku homepage na xtgem, sai ku duba inda aka rubuta START BUILDING ku danna kai, bayan ya gama loading zai kawo wani waje a inda zakuga email, password da dai sauransu.
1. Sai ku shiga inda aka rubuta email, sai ku sa email da kuke aiki dashi
2. Sai ku sauko wajen password, ku saka password naku kar ya kasa haruffa 8 ko nomba takwas
3. Sai kuje repeat password, sai ku maimata password da kuka zaba dazu.
4. Sai ku yi confirming Recaptcha(wato wajen i'm not a robot)
5. Sai ku rubutu username naku wato sunan website naku, misali elguduwis yanzu sabon site namu zai zama "elguduwis.xtgem.com"
6. Sai ku danna signup.
7. Byan ya gama loading zai nuna muku templates wato yadda site naku zai kasance, idan wanda suka nuna muku bai yi muku ba sai ku danna next har sai kunga wanda ya muku, toh sai je kasan template din sai ku danna Confirm and Customized 
8. Bayan ya gama zai nuna muku pick a color preset sai ku duba kalan da zai muku kyau a website naku sai ku zaba dan ya gama zai nuna muku page title, aciki zakuga my personal page sai ku goge ku zabi sunan da zai bayyana idan an shiga site naku.
10. Sai ku danna  Confirm
Shikenan kun bude website naku a xtgem, sai ku shiga website naku.

sai dai kafin wasu su bude site naku sai kunyi confirming email naku, kuduba email inbox naku zakuga sako daga XTGEM sai kuyi confirming email naku

Idan da wata damuwa kuna iya yin comment.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka http://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment