YADDA ZAKU GYARA MEMORY CARD DINKU IDAN YA LALACE


Yau ina so inyi magana ne akan Yadda ake gyara Memory Card  idan ya nuna corrupted ko Error  a sauKake ba tare da anyi amfani da wani Software ba. Da fari kuna bukatar 
Lalataccen Memory Card tare da Card Reader waton gidan saka Memory Card.
Computer
Kafin ku gyara Memory naku

Da farko Ku bude Coputer din ku sai ku danna alamar Windows din Computer, Akwai wajen search sai ku rubuta CMD kuna rubutawa zaka ga ya fito, sai ku budeshi inya bude sai ku rubuta DISKPART Sai ku danna Enter Key na Computer. Zai nuna muku kuna so kuyi installing Na Diskpart, sai ku zabi Yes

Daga nan zai kai ku wani waje sai ka rubuta LIST DISK sai ku danna Enter Key zai nuno muku Disk wato Memory din Computer da kuma lalataccen.
Sai ku duba kuga wannene lalataccen a ciki, Disk 1 ne ko DisK 2 amma yawanci yafi zuwa a DisK 1, sai ku rubuta SELECT DISK 1 sai ku danna Enter Key zai nuna muku DISKPART DisK 1 is now selected, sai ku sake rubuta CLEAN sai ku danna Enter Key idan kuka danna zaku ga ya nuna DisKPart> Succeed Cleaning The Disk. Sai ku sake rubuta CREATE PARTITION PRIMARY sai ku danna Enter Key, zai nuno muku DISKPART> Succeed Creating In The Specified Partition
Sai ku rubuta ACTIVE sai ku danna Enter Key zai nuna maka DISKPART> Marked The Current Partition as Active sai ku rubuta SELECT PARTITION 1 sai ku taba Enter Key zai nuna muku,  Partition 1 is now The Selected Partition sai ku sake rubuta FORMAT FS=FAT32 sai ku danna Enter Key daga nan zai fara Format zaku ga ya Soma  0% to Complete. A haka a hankali har sai ya kai 100%.Shikenan indai anbi yadda yake a rubuce zaka ga yayi successfully.
Madalla Da Karanta Wannan Bayanin Ina farin ciki da ziyartar shifina da akayi. Ga website na wa din kamar haka http://elguduwistechnology.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment